01/12/2023
*IMPORTANT NOTICE!!!*
This is to inform all AFAN family that; Who ever receives a text message from PFAleart (Regarding to NAG-AP Dry Season Wheat Production). Should please leave the sms on his/her phone until his inputs is given to him.
Please don't delete the message because it is genuinely from the Federal Government of Nigeria Under the FMARD).
Signed:
Dr. Imam Umar Nadada,
AFAN Chairman,
Katsina State Chapter.
01/10/2023
Ina taya daukacin shuwagabanni da 'ya'yan kungiyar AFAN tare da sauran Al'umar Nigeria baki daya murnar cikar Najeriya shekara 63 da samun 'yanci.
Ina rokon Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya, Ya kawo mana karshen wannan rashin tsaro da ya addabemu.
Daga karshe Ina taya Manomanmu murna da fatan Nasara a cikin wannan kakar Noma ta shekarar 2023. Tare da fatan samun gwaggwabar riba a cikin abinda muka noma mai amfani.
Dr. Imam Umar Nadada
Shugaban kungiyar AFAN reshen jahar Katsina.
02/09/2023
Ana Umartar daukacin `ya`yan kungiyar AFAN ta jahar Katsina da suyi rejista ta wannan link din domin samun damar shiga gasar Agrivest Reality TV challange
Agrivest Reality TV Challenge Show. Registration is open
https://forms.gle/obiMtQmu5WaYNQEM6
sanarwa:Shugaban Kungiyar AFAN Reshen Jahar Katsina Dr. Imamu Umar Nadada
26/06/2023
Nan ba da jimawaba, zamu kawo maku dauka kai tsaye yanda Babbar Kungiyar Manoma AFAN reshen Jahar Katsina hadin guiwa da Kamfanin taki na Agro dake Jahar Kano zasu kaddamar da rabon bashin takin zamani ga manoma 'yan asalin Jahar Katsina.
Shirin zai gudana a Babban Ofishin Kungiyar dake dab Shatale-talen gidan rodi na Steel Roling anan cikin garin Katsina
Tallafin Lamunin dai za'a badashi ne don ganin an taimakawa manoma masu karamin karfi wanda zai taimakesu suje suyi noma sai bayan sunyi girbi, sun siyar da amfanin gona sannan su biya bashin.
23/05/2023
Hukumar NEPCO ta Kasa Reshen Jahar Katsina ta bayarda tallafin IRI na noman SOBO ga 'ya'yan Kungiyar so6on a kananan Hukumomin Mashi da Kaita.
A ranar Lahadin da ta gabata wanda yayi daidai da 28/05/2023 har Ila yau wannan hukuma ta NEPCO reshen Jahar Katsina a karkashin Jagorancin Alh Kabiru Y Sadoh ta kai daukin tallafin iri na dobo ga Manoman sobo na kananan hukumomin Mashi da Kaita kwana daya bayan da ta raba tallafin iri na Ridi ga manoman ridi na Jahar Katsina, wanda tayi tattaki takanas har wadannan kananan Hukumomi guda biyu.
Yayin kaddamar da jawabin Maraba Shugaban Hukumar Alh. Kabiru Y Sadoh ya shaidawa Al'umma cewar a bincike da ya gabata Jahar Katsina ita ce Jaha ta farko kuma mafi inganci da nagarta wajen noman Ridi da kuma sobo a domin hakannema hukumar tasu ta maida hankali gurin ganin an habbaka noman sobo gadan-gadan a Jahar katsina sannan bayan nazari da bincike sai s**aga yadace su tallafawa Manoma da nagartaccen iri wanda yafi kowane kyau domin samun yabanya mai yawa mai amfani, v SDsannan ya tabbatarwa da manoman cewar da a hankali - a hankali zasu cigaba da kawo masu tallafi kala daban - daban don ganin an habbaka noman ridi a Jahar katsin.
A nasa jawabin Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jahar Katsina Dr. Imam Umar Nadada ya jawo hankalin manoma musamman na karamar hukumar Mashi da su sani cewar Bincike ya nuna a kaf fadin duniya Sobo na kasarmu ta Najeriya yafi na kowace kasa kyau, sannan kuma Sobon Jahar katsina yafi na kowace Jaha kyau a kasarnan, haka zalika Sobon karamar hukumar Kaita yafi na kowace karamar hukumar kyau ( wanda hakan na nufin a duk duniya Karamar hukumar Kaita sunfi ko ina noma Sobo mai yawa kuma ingantacce hakanne yasa shugaban yaja kunnensu da su zabura su dage don ganin sun rike wannan kambu nasu ba tare da barin wasu sun karbeba.
Daga cikin manyan bakin da s**a halarci taron akwai:
Shugaban karamar hukumar Kaita wanda ya samu wakilci,
Shugaban hukumar NEPCO, reshen Jahar katsina,
Shugaban hukumar KIPDECO,
Shugaban Kungiyar AFAN reshen Jahar Kstsina,
Shugaban Kungiyar sobo na Jahar katsina,
Manyan 'yan kasuwa da s**a hada da Alh Yusuf Gafai Katsina
Sarkin Noman Jibia. da sauran shuwabannin Manoma da manoma na jaha da kanaanan Hukumomi da sauransu..
22/05/2023
Hukumar kula da habbaka fitar da kayayyakin noma da sauran albarkatun kasa zuwa kasashen ketare ( Nigerian Export and Promotion Council NEPCO) ta gudanar da rabon tallafin kayan noma da s**a hada da irin sobo, da kuma ridi a ranar Asabar da Lahadin da s**a gabata.
An raba tallafin ridi ga kungiyar Manoman Ridi a ranar Asabar 27/05/2023 a ofishin hukumar kula da kanana da matsakaitan sana'oi ta kasa reshen Jahar Kstsina.
Yayin kaddamar da da shirin bada tallafin Shugaban hukumar NEPCO ya bayyana cewar wannan tallafi yana daya daga cikin shirin hukumar hdin guiwa da gwamnatin tarayya don ganin an tallafawa kananun Manoma musamman anan Jahar katsina
Yayin nasa jawabin Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jahar katsina Dr. Imam Umar Nadada yayi gargadi tare da Nusar da Manoma akan garabasa tare da gwagwgwabar ribar dake tattare da noma ridi, haka zalika ya gargadi Manoma da su kasance masu karfafa junansu kuma su tashi su taimaki kansu domin in s**ai hakan shi zaisa gwamnati ta samu kwarin guiwa wajen taimaka masu.
Haka shima shugaban Hukumar KIPDECO Ahmad Ibrahim Karfi yayi ingantaccen bayani dangane muhimmancin noma ridi sannan yayi masu albishir akan cewar akoda yaushe hukumarsu shirye take don yin hulda da Manoman ridi manya da kanana ya kuma tabbatar masu da Kamfanin da hukumarsu ta tanada don tacewa tare da tsaftace ridi da sanya shi a buhunna da zaa iya daukarshi kai tsaye zuwa kasashen ketare.
Daga karshe wannan taro ya samu halartar manya manyan baki da s**a hada da Shugaban hukumar NEPCO Kabiru Y Sadoh,
Shugaban hukumar KIPDECO Ahmed Ibrahim Karfi,
Shugaban hukumar SMEDAN wanda ya samu wakilci.
Shugaban Kungiyar AFAN reshen Jahar Dr. Imam Umar Nadada da tawagarsa,
Shuwagabannin Kungiyoyin Manoma,
Manoma da sauransu.
15/05/2023
AFAN zata bada tallafin kayan noma bashi ga Manoma dubu goma a duk fadin kasarnan
Ministan Ayyukan Noma da Raya Karkara Dr. Muhammad Abubakar ya kaddamar da shirin bayar da tallafin kayan noma bashi ga Manoma dubu goma a duk fadin kasarnan.
Shirin wanda ya samu kyakkyawan hadin guiwa tsakanin Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa watau AFAN da kuma Fitaccen Kamfanin Kasuwanci na Ghas Integrated Service Limited dake Kano ya samu tagomashi da kyakkyawan tarba daga gwamnatin Tarayya k**ar yanda Ministan Noma ya bayyana a wajen kaddamarwar a ranar Juma'ar da ta gabata a garin Kano.
An dai kaddamar da shirin bayarda tallafin ne da zummar saukakawa Manoma domin gudanar da sha'anin Noma daga cikin yunkurin da gwamnatin tarayya takeyi na farfadowa tare da habbaka Noma da Kiwo a dukkanin sassa da lungunan kasarnan.
Da yake gabatar da bayani a gurin taron Dr. Abubakar ya bayyana cewar bai kyautuba anayin dogaro da fanni guda daya tal wajen habbakar tattalin arzikin kasarnanba, don haka ya k**ata a dukufa wajen kirkiro hanyoyi musamman fannin noma da kiwo kasancewar kasarnan ta ginu da arzikin Noma da kiwo tun kafin zuwan arzikin Man fetur.
Taron ya samu halarta manya manyan Mutane daga Maaikatu daban daban da s**a hada da :
Ministan Noma Dr. Muhammad Abubakar,
Shugabar Inshorar Manoma ta kasa NAIC Folashade Joseph,
Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Manoma ta Kasa Dr. Farouk Rabi'u Mudi,
Shugaban AFAN na Jahar Katsina Dr. Imam Umar Nadada da sauran shuwagabannin Manoma a matakin kasa, Jaha dama na Kananan Hukumomi
29/04/2023
Gargadi Gargadi. Gargadi.
Ana sanar da daukacin manoma na jahar katsina da kewaye cewar akwai wani sabon maganin kwari na feshi wanda hukumar D.S.S ta k**a a a babbar kasuwar Central Market dake cikin garin katsina. Don haka hukumar Aiyukan Gona ta tarayya reshen jahar Katsina ta gargadi manoma da su guji amfani da wannan sabon maganin.
Haka Zalika Hukumar na gayyatar ciyamomi da sakatarori na kowace kungiyar manoma watau Commodities Associtions da su hadu a farfajiyar maaikatar a ranar Laraba 03/05/2023 domin kai ziyarar gani da ido domin tabbatar da abinda 'yan sandan farin kaya na DSS ta sanar sannan kuma a gudanar da zaman meeting domin tattaunawa akan matakin da ya k**ata a dauka dangane da hakan.
Daga karshe kuma AFAN ta kasa ta karyata wani sabon link dake yawo a kafafen sada zumunta na social media wanda ke nuni da cewar AFAN zata bada bashi ga manoma saboda haka ta umurci manoma da su kauracewa wannan link din kasancewar 'yan yahoo ne s**ayi kutse a cikin Manhajar kungiyar
Sanarwa:
FMARD Katsina State
AFAN Katsina State